1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohon ƙundin tsarin mulkin Birtaniya

A kasar Amurka an baje kolin ƙundin tsarin mulkin ƙasar Birtaniya mai suna Magna Carta da aka shirya shekaru dari bakwai da goma da suka gabata.Yayin wannan biki da aka yi garin Sotheby, birnin New York an sayar da kofen wannan ƙundi, dala miliyan ishirin da daya da dubu ɗari uku. Wannan ƙundi da majalisar dokokin Birtaniya ta zartad a shekarar 1297 ya tabbatad da haƙƙin turawan Birtaniya ya kuma sassauta ikon sarakuna.Wani hamshaƙin ɗan kasuwa dake aiki hannu jari mai zaman kansa shine ya sayi wannan ƙundi da nifin adana shi a inda dama yake a gidan tarihin Amurka dake birnin Washington D.C.