Tsohin shugaban Thailand ya ce zai koma gida | Labarai | DW | 25.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsohin shugaban Thailand ya ce zai koma gida

Tsohon shugaban ƙasar Thailand da ke gudun hijira Thaksin Shinawatra ya faɗawa manema labarai cewa ya yi aniyar komawa gida Thailand mai yiwuwa cikin ‘yan makonni masu zuwa bayan da abokan kawancensa suka samu nasara a zaɓen ƙarshen mako. Yace kodayake ya yi niyar komawa ne ya zauna kamar kowane ɗan ƙasa. Thaksin wanda a ka sauke cikin wani juyin mulkin soja a watan Satumba na bara,ana zarginsa ne da laifin cin hanci ,ya baiyana cewa ba zai shiga harkokin siyasa na jam’iyar da ta lashe mafi yawa na kujerun majalisar dokokin ƙasar da aka yi a ranar lahadi ba.Yanzu haka dai jam’iyar tana shirin kafa gwamnatin haɗaka.