1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsibirin Komoro

Shuaibu Othman Sambo March 26, 2008

Dakarun Tarayyar Afrika sun cimma kwato Tsibirin Anjouan

https://p.dw.com/p/DVAE
Tsibirin KomoroHoto: AP

Talatar nan ce sojojin Gwamnatin Comoro tare da hadin gwiwar Dakarun Ƙungiyar Tarayyar Africa suka sami nasarara kwato yankin Anjoun da yan aware karkashin jagorancin Kanar Mohammed Bacar ke rike da shi tun bayan zaben watan Yunin shekara ta 2002.

Tunda da sanyi safiyar ranar Talatan ne dakarun ƙawancen suka ƙarasa gaɓar tsiburin Anjoun inda suka fara ƙwace tasoshin jiragen ruwa da na sama daga hannun 'yan-awaren daga bisani kuma kafin ɗagawar rana suka sami nasarar kwace Matsamudu babban birnin tsiburin daga hannun wasu mayakan sa kai da ke iƙirarin goyon bayan shugaban 'yan awaren kanal Mohammed Baca; wanda kuma ake zaton ya tsere zuwa ɗaya da ga cikin tsiburan da ke maƙwabtaka da Anjouan kuma suke ƙarƙashin ikon gwamnatin faransa domin samin mafaka.

A ranar litinin ɗinnan ce dai shugaba Ahmed Abdullahi Mohammed Sambi na tarayyar tsibirin Comoro ya ba da sanarwar cewa ya amincewa sojojin da su yi duk yanda za su yi tayin anfani da ƙarfinsu domin tabbatar da haɗaɗɗiyar ƙasar, tare kuma da 'yantar da fararen hular da ke zaune a yankin Anjouan.Indai ba a manta ba tun a farkon wannan shekara ce shugaba Ahmed ya bayyanawa taron Ƙungiyar Tarayyar Afurka ƙudiransa na tabbatar da haɗaɗɗiyar ƙasa,inda kuma har ya buƙace ta da ta tallafa masa da dakarunta wajen ganin ya ƙwato ɗaya daga cikin tsuburai ukun da suka haɗu suka yi ƙasar wato Anjouan

daga hannun yan aware.Dr Horf maya Daraktan cibyar nazari kan harkokin da suka shafi Afurka dake Birnin Hamburg ta nan jamus ya kuma yi tsokaci game da wannan mamaya da sojojin Kungiyar Tarayyar Afurka tare da na gwamnatin Comoro sukayi na kwato Anjoun daga hannnun yan Awaren...

"Ina ganin ko mai a bayyane yake tunda daɗewa ƙoƙarin ƙungiyar Tarayar Afurka na sasantawa ya ci tura.Kuma ko a makon jiya Shugaban ƙasar Afurka ta kudu ya yi ƙoƙarin jan hankalin wasu takwarorinsa game da kai hari a wannan yankin na Anjouan;to amma bayan jira na tsawon watanni ba tare da samun wani kyakkyawan sauyi daga ɓangaren yan awaren ba,babu wani sauran zaɓi da ya wuce anfani da ƙarfin sojin."

Dongane da batun ko wannan nasara za ta baiwa dakarun Ƙungiyar Tarayyar Afurka ƙwarin gwiwa da wani sabon matsayi a ƙoƙarin da suke na kwantar da tarzoma da kawo ƙarshen rigimu a sauran ƙasashen Afurka sai ya ce....

"Babu shakka a sauran rigingimun kamar irin na yankin Darfur da Somalia Ƙungiyar Tarayyar Afurka ta gagara yin tasiri.ko da shike idan ka haɗa da tsuburin Comoro zaka ga cewa wannan wuri ne da Ƙungiyar AU ta daɗe tana nuna sha'awarta a harkokin siyasar ƙasar tun sama da shekaru goma.Don haka ya fi masu sauƙi wajen kare martabar ƙasar a matsayin ta na tsitsiya madaurinki guda."

Tsuburin Comoro da ke gaɓar nahiyar Afurka ta sahin kudu maso gabashi ya sha fama da juyin mulki da harin kifar da gwamnati har kusan Ashirin tun daga shekarar 1975 sa'adda ya sami 'yanci daga hannun turawan Faranshi.