Tsibirin Bakassi ya koma Kamaru | Labarai | DW | 14.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsibirin Bakassi ya koma Kamaru

A yau ne Nigeria ta mikawa kamaru tsibirin Bakassi mai albarkatun man petur a hukumance,adangane da zartarwar kotun kasa da kasa ta mdd ,wanda ya kawo karshen rikicin shekaru 13 tsakanin kasashen biyu dake makwabtaka da juna.Ministan sharia na tarayyar Nigeria Bayo Ojo da takwaransa na kamaru Maurice Kamto ,suka rattaba hannu kan takardun yarjejeniyar dake cire ikon tsibirin daga Abuja zuwa yaounde,a wani bukin daya samu halartan jamian mdd dana faransa da Britania da Jamus da kuma na Amurka.Dukkan jamiai da sukayi jawabi a wajen bukin,sun jaddada bukatar bangarorin biyu su darajawa yarjejeniyar da aka cimma akan tsibirin na Bakassi.

 • Kwanan wata 14.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5v
 • Kwanan wata 14.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5v