1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsauraren matakan tsaro a Abuja

October 17, 2010

A wani shirin ko ta kwana, a Najeriya jami'an tsaron sun bazu cikin birnin Abuja, inda ƙungiyar MEND ta yi barazanar kai hari.

https://p.dw.com/p/Pg3B
Majalisar dokokin tarayya da dutsen Aso Rock, a Fadar gwamnatin NajeriyaHoto: DW

A Najeriya jami'an tsaron sun tsaurara matakan tsaro a babban birnin ƙasar Abuja, bayan da ƙungiyar da takai harin ranar bikin samun 'yancin kan ƙasar, ta sake yin barazanar kai wani harin. Rohotonni sukace anga 'yan sanda masu kunce bama bamai, na bincikar ababen hawa musamman a kusa da filin jiragen sama dake Abuja, inda sai an binciki dukkan motar da za ta fita ko shiga filin jigin saman. Wani matafiyi a Abuja, yace shi kam bai taɓa ganin irin tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka, kama daga jiya ba. A ranar Juma'a ne dai ƙungiya karen 'yan yankin Niger Delta wato MEND, ta ce za ta sake kai wasu hare-haren bama bamai, kamar waɗanda ta kai a Abuja ranar da aka yi bikin samun yancin kan ƙasar na shekaru 50.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu