1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaurara matakan tsaro a Pretoria

Yusuf Bala Nayaya
February 21, 2017

Kasar Afirka ta Kudu da ke da matsalar marasa aikin yi da ta kai kashi 25 cikin dari ta shiga rudani, inda ake samun tashin hankali nan da can saboda zargin baki da mamaye arzikin kasar.

https://p.dw.com/p/2Y0bP
Südafrika Pretoria Studentenproteste Ausschreitungen
Hoto: Reuters/S. Sibeko

Matakin kara karfafa tsaron dai na zuwa ne bayan da aka samu wasu bata gari da suka fasa shaguna masu tarin yawa da ke zaman mallakar baki 'yan kasashen waje, tare da sace kayayyaki da ke jibge cikin shagunan kamar yadda kafafan yada labarai da ma shedun gani da ido suka tabbatar.

Kasar Afirka ta Kudun dai na da matsalar marasa aikin yi da yawansu ya kai kashi 25 cikin 100. Al'ummar wannan kasa na nuna yatsa ga baki 'yan kasashen waje a matsayin matsala da ke zama sila ta hana musu samun aiki a kasarsu ta haihuwa. A cewar wasu rahotanni dai tun a daren ranar Litinin ne aka samu wasu suka dira shagunan na baki inda suka wawashe abin da ke ciki bisa zargin cewa wai wurare ne da ake ajiye kayan laifi.

Kasar ta Afirka ta Kudu dai na da baki da yawansu ya kai miliyan biyu da dubu 400, kamar yadda kididdigar kungiyar kasa da kasa mai kula da baki ta bayyana.