1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaurara matakan tsaro a kasashen Turai

Salisou BukariJanuary 16, 2015

Tun bayan harin da aka kai a kamfanin mujallara Charlie Hebdo ta kasar Faransa , sauran kasashen Turai kamar Beljiyam, da Jamus, sun dauki kwararan matakan tsaro.

https://p.dw.com/p/1ELkP
Angela Markel in Berlin 22.10.2014 Symbolbild USA Deutschland Beziehungen
Hoto: Getty Images/AFP/Odd Andersen

A halin yanzu dai, hukumominn kasar Beljiyam sun ce a shirye suke su yi kira ga sojojin kasar wajan samar da tsaro a cewar Firaministan wannan kasa Charles Michel, alhali kuwa har kawo yanzu a wannan kasa sojoji basa cikin masu aikin kwantar da tarzoma.

Bayan samaman da jami'an tsaro na musamman masu yaki da ta'addanci suka kai a jiya, majalisar ministocin wannan kasa ta yi wani zaman taronta kan wannan batu, inda kuma ta dauki wasu matakai a kalla goma sha biyu da zasu karfafa yaki da ta'addancin da wannan kasa ta runguma. Valeur Thierry na ofishin ministan shari'ar kasar ya yi tsokaci kan binciken da suka aiwatar a wuraren da suke zargi.

"Binciken da muka aiwatar a gidajan wadannan mutane, munyi shi ne bisa wasu dalillan rahotanni da muka samu kan wata kungiya da ta hada da wasu wadanda suka dawo daga Siriya, kuma binciken ya nunar cewa wadannan mutane suna da aniyar aiwatar da manyan hare-hare cikin wannan kasa ta Beljiyam kuma ba da dadewa ba."

Belgien Anti-Terror-Einsatz in Verviers 15.01.2015
Hoto: Reuters/Stringer

A yammacin ranar Alhamis ce kuma, gwamnatin ta Beljiyam ta kara tsaurara matakan tsaro na musamman da suka shafi kaf fadin wannan kasa, duk kuwa da cewa babu wata barazana tabbatacciya da ake da ita ta kai hari a cewar Firaministan Charles Michel:

"Bamu da wata masaniya kan wata barazana ta musamman, to amma ganin yanayin da ake ciki, dole ne mu kara daukan matakan rigakafi a fannin tsaro, sabili da haka akwai kwararan matakai da zamu dauka kuma bisa dalillai na tsaro ba zamu sanar da su ba."

Bayan dai kasar Beljiyam, a nan Jamus ma dai, hukumomin tsaron kasar sun dauki nasu matakai, inda jami'an tsaro na 'yan sanda a kalla 250 suka kai wani samame cikin su kuwa har da jami'ai na musamman, inda suka shiga binciken wadanda ake ganin Musulmai ne masu tsatsauran ra'ayi a Berlin, jami'an sun shiga cikin gidaje 12 da ake zargin suna kumshe da wadannan mutane, kuma an kama mutum biyu daga cikin wadanda ake zargi, sannan zasu ci gaba da bincike kan wasu da ake wa wannan zargi.