Tsaurara matakan tsaro a Jamus | Labarai | DW | 07.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsaurara matakan tsaro a Jamus

Jamian sashin tsaro dake nan tarayyar Jamus,sunyi kira ga gwamnati data haranta horarrwa a sansanonin yan tarzoma ,adangane da yunkurin kai hari da aka gano ,wanda kuma aka dangane da wasu yan tarzoma da suka samu harswa a kasar Pakistan.Wannan kiran dai yazo ne adadidai lokacin da hukumomin kasar ke cigaba da gudanar da bincike akan mutane da dama ,wadanda ake zargi da tallafawa mutane ukun da aka cafke akan zargin shrin kai harin a ranar talata.A yanzu haka dai ana gudanar da bincike a kann wasu mutane guda 7,wadanda daga cikinsu biyar sanannu ne wa yansanda,,inji kakakin pfishin gurfanar da kara na tarayya Andreas Christeleit.Wannan hali da ake ciki dai ya jagoranci kiraye kiraye,adangane da bukatar daukan tsararan matakan tsaro,a wannan kasa da ke da tsauraran dokoki da suka shafi rayuwar mutane.