1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaro ya ta'azzara a kan iyakar Nijar da Mali

Abdoulaye Mamane Amadou MA
April 23, 2018

Masanan tsaro da kungiyoyin kare hakki a Jamhuriyar Nijar, sun damu da yanda sannu a hankali masu rike da makamai don kare kai ke rikida zuwa masu kisar gayya tsakanin kabilun da ke zaman tare da iyakokin kasar da Mali.

https://p.dw.com/p/2wXAj
Kokarin tabbatar da tsaro a tsakanin Nijar da MaliHoto: Getty Images/AFP/P. Guyot

Da fadin kilomita fiye da 820 galibi na hamada da manyan tsaunuka, Jamhuriyar Nijar dai na raba iyaka mafi tsawo da fadi da makwafciyarta kasar Mali daga Yamma, hakan da ma arewa maso yammacin kasar. Sai dai tun daga lokacin da arewacin kasar Mali ya fada hannun masu tayar da kayar baya a shekara ta 2011, matsalolin tsaro suka kara tabarbarewa a iyakokin kasashen biyu. Lamarin ya kai jama’ar da ke zaune a yankunan musamman ma Fulani da Abzinawa daukar miyagun makamai walau don kare kansu ko na kuma tarin arzikin da Allah ya albarkanci yankin da shi. Ko da yake ba tun yau ba aka ake zaman doya da manja tsakanin kabilun yankunan kasashen biyu masu kallon al’amura ta fuskar tsaro.

Mali - Französische und malische Truppen töten in Mali 30 Dschihadisten
Hoto: Getty Images/AFP/D. Benoit

Wani abin da ya auku a baya bayan nan mai nasaba da bazuwar makamai a yankunan biyu dai shi ne wasu da ke dauke da makamai sun hallaka mutum akalla 7 a yankin Filingue mai makwaftaka da Malin, kamar yanda Abdoulaye Bagasa dan jarida a garin ya tabbatar wa DW.

 

Ko baya ga lamarin da ya auku a garin na Filingue, batun sace dan kasar Jamus din nan da ke aikin agaji kan hanyarsa ta fitowa daga Innatas a kwanakin baya da kawo i yanzu ba a san ko su wane ne ba suka yi a yankin na Tillaberi, na daga cikin abubuwan da ke kara tabbatar da cewar karara matsalar makamai na ci gaba da daukar sabon salo. Sai dai ga masu sharhi kan lamuran tsaro ire irensu Laouali Aboubakar, cewa suke kamata ya yi hukumomin Nijar su bude wani sabon babi na tattauanwa da mazauna yankunan karkara. Wasu rahotanni na cewar yanzu hakan askarawan kasashen na Mali da Nijar na ci gaba da sharar dajin iyakokin biyu don kakkabe masu dauke da makamai da kuma ke addabar yankin.