Tsaro: Jamus za ta bawa Nijar tallafi | Siyasa | DW | 03.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tsaro: Jamus za ta bawa Nijar tallafi

Tarayyar Jamus ta ce za ta tallafawa Jamhuriyar Nijar wajen ganin sha'anin tsaro ya inganta a daidai lokacin da makwatan kasar ke fama da kalubale na 'yan tada kayar baya.

Wannan tallafi da Jamus din ta ce za ta bada na zuwa ne daidai lokacin da ministocin kasahen Fransa da Tarayyar ta Jamus ke ziyara a Nijar din wadda ake kallo a matsayin irinta ta farko a tarihi da ta hada wasu manya-manyan kasashe biyu da suka ziyarci Nijar da manufa guda. Muhimman batutuwan da suka mamaye ziyarar su ne na tsaro musamman ma tallafin da kasashen za su iya kawowa kasar Nijar da ke zagaye da kasashen da ke fama da 'yan ta'adda sai kuma batun bunkasa karkara da kuma matsalar bakin haure.

Niger Frank-Walter Steinmeier in Niamey

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier da takwaransa na Faransa Jean Marc-Ayrault lokacin da suka isa birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar

Ministan harkokin wajen Nijar Alhaji Ibrahim Yacouba ya ce ''sun nuna cewa za su cigaba da taimakawa Nijar kan abubuwn da suka dameta ciki kuwa har da nemarwa al'umma abinci da sauran muhimman abubuwa.'' Ministocin sun kuma dauki alwashi taimakawa ta kowane fanni domin ganin tsarin da tuni aka san kasar ta Nijar da shi ya tabbata shi ne zaman lafiya mai dorewa. Ministan Harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya ce ''muna talafawa cigaban kwanciyar hankalin kasar Nijar dama yankin baki daya ta fannoni daban-daban ciki kuwa har da tsaro.''

Kasashen Jamus da Faransa dai na talafawa Nijer da makudan miliyoyi na CFA wajan bunkasar fannoninta na noma da kiyo ganin cewar fannin na daya daga cikin abubuwan da kasar ta ke dogaro da shi kamar yadda ministan harkar noma da kiwo na kasar Alhaji Albade Abouba ya shaidawa DW. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Jamhuriyar Nijar ke jiran tallafin kasashen Turai ne da na euro miliyan 1 don dakile barazanar 'yan ci rani da bakin haure.

Sauti da bidiyo akan labarin