Tsarin agaji na ƙungiyar EU na tsaida darajar takardun kuɗin Euro | Labarai | DW | 10.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsarin agaji na ƙungiyar EU na tsaida darajar takardun kuɗin Euro

Ƙungiyar Tarayya Turai ta kafa wani asusun tallafi na kuɗi domin taimakawa ƙasashen ƙungiyar da ka iya samun matsala ta kuɗi

default

Tutar EU haɗe da na sauran ƙasashen ƙungiyar

Wakilai na ƙungiyar Tarayya Turai daga ƙasashe 27 da suka kammala taro a jiya a birnin Brussels sun amince da kafa wani asusun tallafi na kuɗi da ya kai miliyan dubu 750 na kuɗin Euro, domin hana bazuwar matsalar tattalin arziki a cikin sauran ƙasashen ƙungiyar da ka iya tasowa.

Tsarin wanda zai taimaka ga kare darajar kuɗin Euro, ya biyo bayan matsalar tattalin arziki da ƙasar Girka ta yi fama da ita, wacce ta yi barazana ga dagula al'amuran kuɗi a nahiyar Turai baki ɗaya.

Kashi na farko na kuɗaɗen da ya kai miliyan dubu 60 na Euro zai fito ne daga asusun ƙungiyar sannan miliyan dubu 440 na gudunmuwar ƙasashen ƙungiyar Tarayya Turai daban daban, wanda kuma zai samu ƙarin miliyan dubu 250 na Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF. A cikin asusun ne dai za a riƙa baiwa ƙasashen ƙungiyar da ka iya samun matsalar kuɗin tallafin.

Bayan kammala taron Ministan kuɗi na ƙasar Autriya Josef Pröll ya ce:

"Yanzu wani lokaci ne mawuyaci ga takardun kuɗin na Euro har ma ga manufofin ƙasashen Turai.

Haƙiƙa yanzu wani hali mafi tsanani ne aka shiga a cikin shekaru da dama to amma bai gagaremu warware ba."

Su ma dai manyan Bankuna na nahiyar Turai sun kawo na su ɗauƙi a cikin wannan yunƙuri da za su baiyana kason da za su bayar a nan gaba.

Mawallafi: Abdurrahmane Hassane

Edita: Mohammad Nasiru Awal