1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsare babban jami'i a majalisar mulkin sojin Nijar

October 14, 2010

Majalisar koli ta mulkin sojin Nijar ta sanar da cafke Kanal Abdoulaye Badie domin amsa tambayoyi

https://p.dw.com/p/PeLq
Hoto: AP

Wata majiyar sojin jamhuriyyar Nijar ta sanar da cewar, hukumomin sojin kasar, sun tsare mataimakin jagorar majalisar koli ta mulkin sojin kasar Kanal Abdoulaye Badie a hedikwatar sojoji da ke Niamey babban birnin kasar. Majiyar ta kara da cewar, tun a jiya ne ake tsare da Kanal Badie, domin yi masa tambayoyi, amma ba tare da bayyana dalilan tsare shi ba. Badie ya kasance babban magatakarda ne a majalisar koli ta mulkin sojin kasar, wadda ke karkashin jagorancin Janar Salou DJibo daya hambarar da gwamnatin shugaba Tandja Mamadou a cikin watan Fabrairu.

A ranar Lahadin da ta gabata ce Djibo ya sanya hannu akan dokar sojin da ta soke mukamin babban magatakarda, amma ya kyale Badie ya ci gaba da zama mamba a majalisar koli ta mulkin sojin. Hakanan a ranar Jumma'ar da ta gabata ce Janar Djibo ya sallami kwamandan rundunar kasar Laftana Kanal Abdou Sidikou, amma sanarwar ba ta bayar da dalilin daukar matakin ba.

Tsarewar da hukumomin sojojin Nijar suka yiwa tsohon babban sakataren majalisar dai, ta zo ne a dai dai lokacin da kasar ke shirye shiryen komawa ga bin tafarkin dimokradiyya, inda za'a gudanar da kuri'ar raba gardama akan sabon tsarin mulkin kasar a ranar 31 ga watan Oktoba, kana da gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 31 ga watan Janairu 2011. A ranar shidda ga watan Afrilun 2011 ne sojojin za su mika mulki ga zababben shugaban kasa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Halima Balaraba Abbas