Tsanantar tashe tashen hankula a Iraqi | Labarai | DW | 07.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsanantar tashe tashen hankula a Iraqi

Sojin Amurka a Iraqi sun sanar da rasuwar sojin su daya, wasu uku kuma a cewar su sun samu raunuka. Al´amarin ya faru ne bayan tashin wani bom a kudancin birnin Bagadaza . Ko da a arewacin kasar ta Iraqi sai da mutane biyu suma suka rasa rayukan nasu, wasu kuma 12 suka jikkata.A can ma yankin Kirkuk, bayanai sun sanar da tashin wasu bama bamai, wanda sanadiyyar hakan mutum daya ya rasa ransa wasu 11 suka jikkata. Wadannan tashe tashen hankula na faruwa ne a yayin da kasar ke neman bakin zaren warware rikice rikice dake addabar kasar ne.A daya hannun,wasu daga cikin manya manyan shi´awa a kasar sun amince da hada hannu da hannaye don kawo karshen zubar da jini a kasar.Moqtadar Al Sadr da Abdul Aziz Al Hakim, sun dauki wannan matakin ne, don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu a game da burin da aka sa a gaba.