1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsananin zafin rana ya halaka mutane da dama a kudu maso gabashin Turai

July 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuFa

Rashin kyawon yanayi na addabar nahiyar Turai gaba ki daya. A halin ruwa ya malale daukacin yankin tsakiya da yammacin Ingila a daidai lokacin da Birtaniyar ke fama da masifar ambaliyar ruwa mafi muni a cikin shekaru 60. Koguna da dama ciki har da na Severn da Thames na fuskantar barazanar batsewa. Sabanin haka a kudu maso gabashin Turai zafin rana da ake fama da shi ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane a kasashen Hungary, Romania, Bulgariya da Girika. Babban jami´in kiwon lafiya na kasar Hungary Ferenc Falus ya ce mutane 500 suka rasa rayukansu sakamakon zafin rana da aka kwashe mako guda ana fama da shi a kasar.