Tsamin dangantaka tsakanin Rasha da Georgia | Labarai | DW | 02.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsamin dangantaka tsakanin Rasha da Georgia

Ana cigaba da zaman tankiya tsakanin Rasha da maƙwabciyar ta ƙasar Georgia. Rahotanni na baya bayan nan na cewa shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin, ya soki lamirin Georgia dangane da tsare wasu sojin Rashan huɗu bisa zargin leƙen asiri. A wata sanarwa bayan taron majalisar tsaro ta ƙasar, Putin ya baiyana kama sojojin da Georgia ta yi da cewa taáddanci ne. Ya kuma danganta shugaban ƙasar Georgian da tsohon shugaban hukumar yan sandan ciki na tsohuwar tarayyar Soviet Lavrenty Beria wanda ya hallaka miliyoyin farar hula na tarayyar Soviet a tsakanin shekarun 1930 zuwa 1940. A kuma halin da ake ciki, Rasha ta kammala kwashe dukkan maíkatan ta daga ofishin jakadancin ta a Tblisi babban birnin ƙasar Georgia, bugu da ƙari, ta kuma dakatar da yarjejeniyar da suka cimma a baya, na janye sojojin ta daga Georgia.