Tsugunne ba ta kare ba
November 17, 2015Talla
Ranar Juma’a (17-11-2015) Zamu kawo muku kashi na karshe na shirinmu na Tsaka Mai Wuya, wanda muka kawo muku a zubi har hudu dangane da rayuwar matasan nan Hauwa, Nasir da Ado wadanda muka bibiyi irin kalubalen da suke fiskanta yau da kullun. Mun dai ji irin matsalolin da Hauwa da Nasir suka rika fiskanta a rayuwar aure musamman saboda kyawar cutar da ya ke dauke da ita, kuma mun ga yadda al’ummar Makera ta shiga wani yanayi sakamakon ambaliyar ruwan da ta ci mutane. Mahaifin Ado na daga cikin wadanda ba a gani ba, anya za’a samo bakin zaren kuwa? Sai ku kasance tare da mu dan jin yadda za’a karasa….taken shirin dai shi ne – „Dan marayan zaki"