Tsaikon kafa ministocin Jamhuriyar Nijar | Siyasa | DW | 08.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tsaikon kafa ministocin Jamhuriyar Nijar

An fara nuna damuwa da jinkirin da ake samu wajen nada sabbin ministocin gwamnatin Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar.

A Jamhuriyar Nijar an fara nuna damuwa kan lokacin da ake dauka kafin nada sabbin ministocin kasar. Tun bayan rantsar da Shugaba Mahamadou Issoufou a wa'adin mulki na biyu a karfon wannan wata na Afrilu ya sake nada Brigi Rafini a masayin firaminista, amma kawo yanzu aka ji shiru bisa nada sabbin ministoci.

Tuni kungiyoyin fararen kula da 'yan gwagwarmaya suka fara nuna damuwa kan jinkirin da ake samu, wajen nada ministocin a cikin gwamnatin ta Shugaba Issoufou.

Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012

Firaminista Brigi Rafini na Jamhuriyar Nijar

Jamhuriyar Nijar tana daya daga cikin kasashen da ke sahun gaba na nahiyar Afirka masu fuskantar kalubale iri-iri saboda hakan mayar da hankali ga tarin matsalolin da take a ciki na daga manya-manyan fatar da masharhanta ke yi ga sabuwar gwamnatin da za ta jagoranci kasar maimakon cece kuce irin na siyasa, Alhaji Moustapha Kadi Oumani na daga cikin wadanda ke ganin lokaci ya yi da 'yan siyasa za su ji tausayin kasar.

Ya zuwa yanzu dai sabuwar majalisar ta ministocin na a matsayin mace ce da ciki ganin irin yanda wasu ke ta fatar shigar 'yan adawa a ciki domin gina kasa masu sharhi na masuganin shigar 'yan adawa zai kara haifar da wasu rarrabuwa da cece kuce a fagen siyasar kasar. Yayin da a share daya Shugaba Issoufou ya samu goyon bayan jam’iyyun siyasa sama da 50 wadanda wasu ke ganin tilas bisa al’ada kowace jam’iyya sai an yi mata tukuici irin na rabon mukami, sai dai takan yi wu a na tsamanin wuta makera sai ta bulla a masaka kamar yanda wani mai sharhi a fagen siyasa ya bayyana wa DW.

Sauti da bidiyo akan labarin