1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaiko ga ficewar Birtaniya daga kungiyar EU.

January 24, 2017

Kotun kolin Birtaniya a yau Talata ta yanke hukuncin cewa wajibi ne gwamnatin ta nemi amincewar majalisar dokoki kafin ta fara shirin janye kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai.  

https://p.dw.com/p/2WJZe
Großbritannien Gina Miller Urteil des Obersten Gerichts zu Brexit
Hoto: Getty Images/L. Neal

Kotun kolin Birtaniya ta ce gwamnatin ba za ta iya fara amfani da kudirin doka ta 50 domin ficewar ba sai ta nemi amincewar majalisa dokoki a cewar babban alkalin kotun David Neuberger 

Kotun ta ce janyewar Birtaniya daga EU za ta haifar da sauye sauye a dokokin cikin gida a saboda haka akwai bukatar a tuntubi majalisa.

Hukuncin dai na zama koma baya ne ga shirin Firaminista Theresa May na fara shirin janyewar Birtaniyar a karshen watan Maris. Babban lauyan gwamnatin Ingila da kuma Wales Jeremy Wright yace basu da wani zabi face yin biyayya ga umarnin kotu

Yace gwamnati za ta yi biyayya ga hukuncin kotu za kuma ta yi dukka abin da ya wajaba na aiwatar da umarnin, A tsawon wannan shari'a kotu ta fayyace cewa ba yanke hukunci ta yi akan dacewa ko akasin haka na ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai ba. Al'ummar Birtaniya sun riga sun yanke hukunci a zaben raba gardama, yanzu batu ne na siyasa ba na shari'a.