Tsaiko a ƙidayar zaben Kenya ya janyo tarzoma | Labarai | DW | 30.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsaiko a ƙidayar zaben Kenya ya janyo tarzoma

A ƙasar Kenya tsaiko da aka samu wajen ƙirga kuri’u a zaɓen da aka gudanar ranar alhamis ya haddasa tarzoma,inda wasu mutane uku suka rasa rayukansu yayinda magoya bayan shugaban adawa Raila Odinga suke zargin gwamnati da yin maguɗin zaɓe. Tun da farko an sanar da cewa Odinga ya samu kuri miliyan 3 da dubu ɗari takwas da tamanin da takwas yayinda Kibaki ya samu kuriu miliyan uku da dubu ɗari takwas da arba’in,tana mai baiyana ƙirga kashi 90 cikin ɗari na kuri’u daga mazaɓu 180 cikin mazaɓu 210. ‘yan sanda sun ce an harbe wani dan zanga zanga a garin Migori a yammacin Kenya,jamian tsaro kuma sun harbe wasu biyu a yankin Eldoret. Masu sa ido na Ƙungiyar Tarayar Turai da Amurka tun farko sunce zaben ya gudana salin alin.