Tsagerun Niger Delta sun sake mutane 24 da suka sace,bayan makoni uku. | Labarai | DW | 13.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsagerun Niger Delta sun sake mutane 24 da suka sace,bayan makoni uku.

A yau talata ne 'yan bindiga a yankin Niger Delta sun saki yan kasan Filipin su 24 da suka kame a watan da ya shege.

Shugabar kasar Filipin Gloria Arroyo ta yaba da kokarin gwamnatin Nigeria da yin hakan.

Yan bindigan sun mika mutanen ne hannun sakatarin gwamnatin jihar Delta Ovie Omo-agege.

Amma har yanzu ba a bayyana batun machen cikinsu da aka sace ba.