Tsagerun matasa a Ivory Coast sun kara kai wani sabon hari | Labarai | DW | 19.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsagerun matasa a Ivory Coast sun kara kai wani sabon hari

Tsagerun matasa magoya bayan shugaba Lauret Gabgbo sun kara kaiwa jami´an Mdd a birnin Abijan a kasar Ivory Coast hari.

Wannan dai hari na yau yazo ne a dai dai lokacin da kwamitin sulhu na Mdd ke tunanin kakabawa kasar takunkumi.

Tsagerun matasan dai sun ci gaba da gudanar da zanga zangar ne a rana ta hudu, duk kuwa da kiran da Shugaba Lauret Gbagbo na kasar da shugaba Obasanjo na Nigeria suka yi musu na daina tada zaune tsaye a kasar.

Kafin dai kai wannan hari , bayanai daga birnin sun nunar da cewa an bude wasu shaguna na saye da sayarwa a birnin to sai dai ba kamar yadda yake ada ba.