1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta kan rikicin Siriya ta kawo karshe

October 22, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta gaza kwashe fararen hula daga birnin Aleppo har zuwa karshen wa'adin tsagaita wuta kan rikicin Siriya.

https://p.dw.com/p/2RZA7
Syrien Aleppo Bergung Verletzte Helfer
Hoto: picture alliance/AA/A. al Ahmed

A wannan Asabar tsagaita wutar da dakarun gwamnatin Siriya da tallafin  Rasha ke kawo karshe a birnin Aleppo, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa ta gaza kwashe fararen hula da rikici ya ritsa da su a daga cikin birnin.

Mahukuntan Rasha suka tsagaita wutar zuwa yammacin wannan Asabar, amma babu kara wa'adin duk da roko daga Majalisar Dinkin Duniya. Kafofin yada labaran gwamnatin Siriya gami da mahukuntan Rasha sun zargi 'yan tawaye da hana fararen hula ficewa daga birnin na Aleppo, inda suke amfani da su a matsayin garkuwa.

A wani labarin kimanin mutane 150 suka yi zanga-zanga a birnin London na kasar Birtaniya da suke neman ganin an dauki matakan da suka dace domin kawo karshen rikicin na Siriya.