Tsafin yan tawayen Cote D` Ivoire sun gama belin pirsinonin yaƙi | Labarai | DW | 27.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tsafin yan tawayen Cote D` Ivoire sun gama belin pirsinonin yaƙi

Tsafin yan tawayen FN na ƙasar Cote d`Ivoire, sun bayyana belin dukkan pirsinonin yaƙin da ke cikin hannun su.

Tsafin yan tawayen FN, sun yi belin sojoji 3, na rundunar gwamnati, wanda su ka capke yau da shekaru 2 da su ka gabata.

Kamar yadda yarjejeniya da gwamnati da ƙungiyar FN, ta tanada, bayan sakin wannan sojoji ,za a girga rundunar haɗin gwiwa, da za ta ƙunshi dakarun gwamnati da tsanfin yan tawaye.

Wakilin ƙungiyar Red Cross Antoine Gran,da ya halarci bikin sakin sojojin 3, ya tabbatar da cewa, a halin yanzu babu pirsinan yaƙi ko ɗaya, daga ɓangarorin 2.

Daga cimma yarjejeniya a watan maris zuwa yanzu, an yi belin jimmilar mutane 110.