1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Trump shugaban Koriya ta Kudu

Gazali Abdou Tasawa
May 22, 2018

Shugaba Donald Trump na Amirka zai gana a wannan Talatar da takwaransa na Koriya ta Kudu Moon Jae-in na Koriya ta Kudu domin tattauna batun ganawar da za ya yi a watan gobe da Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa.

https://p.dw.com/p/2y5VZ
USA Donald Trump im Weißen haus in Washington
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Vucci

Shugaba Donald Trump na Amirka na ganawa a wannan Talata da takwaransa Moon Jae-in na Koriya ta Kudu domin tattauna batun ganawar da aka shirya za a yi a watan gobe tsakanin Donald Trump din da Shugaba Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa ganawar da kuma ke cikin halin rashin tabbas a halin yanzu. 

Lokacin da ya rage makonni uku shugabannin kasashen biyu su yi wannan haduwa mai cike da tarihi a Singapour, Shugaba Trump na bukatar canza yawu ne da takwaransa na Koriya ta Kudu domin ya taimaka masa ga fahimtar manufofin da ke tattare da shugaba Kim Jong Un a game da wannan haduwa tasu. Batun dakatar da shirin nukiliyar Koriya ta Arewar baki daya dai na a sahun gaban muhimman batutuwan da shugabannin kasashen biyu za su tattauna a haduwar tasu. 

A makon da ya gabata ne dai Koriya ta Arewar ta yi barazanar soke shirin ganawar shugabannin kasashen guda biyu domin nuna rashin amincewarta da yadda Amirkar ke son ganin ta yi watsi da shirin nukiliyar tata kamar yadda kasar Libiya ta yi da nata a loakcin mulkin marigayi kanal Gaddafi, abin da Koriya ta Arewar ke cewa ba za ta sabu ba.