Trump: ′Yan jarida ba su da gaskiya | Siyasa | DW | 23.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Trump: 'Yan jarida ba su da gaskiya

Shugaban Amirka Donald Trump ya ce kafofin yada labarai ba su fadi gaskiya dangane da yawan mutanen da suka halarci bikin rantsar da shi a ranar Jumma'a ba.

Sama da mutane miliyan biyu ne dai suka yi tururuwa zuwa biranen Amirka, a dai-dai lokacin da mata ke gudanar da gangamin adawa da kaskanci da Trump ya yi musu.

Fitattun mata a fannoni daban-daban da masu fafutukar 'yanci ne dai suka yi dafifi a birnin Washington, a daidai lokacin da Trump ya zargi kafofin yada labarai kan abin da ya kira rashin gabatar da rahotannin gaskiya game da yawan wadanda suka halarci bikin rantsar da shi a ranar Jumma'ar da ta gabata ba. Sabon shugaban na Amirka bai ce uffan game da wannan gangamin adawa ba, wanda ke zuwa  a ranarsa ta farko akan madafan iko.

Duk da cewar babu cikakkun alkaluman wadanda suka shiga wannan zanga-zangar lumana,  wadanda suka shirya sun ce sama da mata miliyan guda ne suka hallara a birnin washinton kadai, daura da wasu kimanin 600 da ake gudanarwa a sassa daban-daban na duniya. Matan wadanda suka hada da 'yan makaranta sun jaddada cewar wajibi ne a daraja 'yancin mata.