Trump ya yi Allah wadan kiran sake kidayan kuri′u | Labarai | DW | 27.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya yi Allah wadan kiran sake kidayan kuri'u

Zababben shugaban Amurka ya na martani ne dangane da karuwar kira da a sake kidayan kuri'u da aka kada a wasu jihohi guda uku a zaben shugaban kasa da ya gudana ranar 8 ga watan Nuwamba.

Wannan shi ne karon farko da Trump ya yi martani kan kalubalantar sakamakon zaben, duk da cewar ya na cigaba da nada mukamai bayan nasarar ba-zata da ya samu.

Hamshakin mai kudin na birnin New York wanda ya sha yin ikirari game da yiwuwar arongizon kuri'u a bangaren abokiyar takararsa Hillary Clinton gabanin zaben, ya bayyana sabon yunkurin da kasancewa bita-da-kulli ne kawai ake wa nasarar da ya samu.

Trump ya sha kawar da kai dangane da kalaman dan takarar jam'iyyar kare muhalli Jill Stein, na bukatar sake waiwayen kuri'un da aka kada a jihohin Wisconsin da Michigan da Pennsylvania.