Trump ya tattauna da Buhari kan ta′addanci | Labarai | DW | 14.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya tattauna da Buhari kan ta'addanci

Shugaban Amirka Donald Trump ya ce kasarsa a tsaye take ta bada sabbin makamai ga gwamnatin Muhammadu Buhari ta Najeriya a yakin da take yi da 'yan ta'adda.

Shugaban Amirka Donald Trump ya amince cewa kasarsa za ta tallafa wa Najeriya a yakin da take yi da ta'addanci. Mai magana da yawun shugaban ya bayyana haka a shafinsa na Twitter biyo bayan tattaunawa ta waya da aka yi tsakanin shugabannin biyu Amirka da Najeriya a ranar Litinin.

A cewar bayanan Garba Shehu, Amirka a tsaye take ta bada sabbin makamai ga gwamnatin ta Najeriya a yakin da take yi da 'yan ta'adda. Har ila yau Amirkar ta gayyaci Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar don ya kai wa gwamnatin ta Shugaba Trump ziyara zuwa birnin Washington. Shugaba Buhari dai ya je birnin London na Birtaniya don duba lafiyarsa tun a watan Janairu.

Karkashin tsohuwar gwamnatin Amirka ta  Barack Obama, Amirka ta ki sakin jiki baki daya ga batun kulla yarjejeniyar makamai da sojan Najeriyar ta yiwu saboda dalilai na cin hanci da rashawa da ma batun take hakki na bani Adama. Duk kuwa da kasancewar kasar mai bukata ta makaman da zata yaki mayakan Boko Haram da ayyukansu suka halaka dubban al'umma a kasar.