1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya soke dokar kasuwancin TPP

Kamar yadda ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabe ranar farko da ya shiga ofishinsa shugaban kasar Amirka ya sa hannun soke yarjejeniyar kasuwancin bai daya da wasu kawayenta.

Ranar aiki ta farko bayan ranzuwarsa, Shugaban kasar ta Amirka Donald Trump, ya fara aiwatar da mahimman alkawura da ya yi a lokutan yakin neman zabe. Inda ya sa hannu kan wasu ayoyin doka. Daga cikin dokar da aka soke, har da kasuwancin bai daya, wanda aka cimma a tsakanin Amirka da wasu kawayenta, yarjejeniyar wace aka sani da TPP, kana ya sa hannu domin soke kudin gwamnatin Amirka ke baiwa kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda ke bada tallafi a kasashen waje ga ayyukan zubar da ciki. Sabon shugaba Trump, ya kuma bada goron gayyata ga Firimiyar Birtaniya Threasa May, wace za ta kawo ziyara a ranar Juma'a mai zuwa. Wannan dai ita ce ranar farko ta aiki, bayan ranzuwar Trump a matsayin shugaban kasa. Sa hannun kan wadannan ayoyi da ya soke su a yau Litinin, ya kara tabbatar cewa sabon shugaban na Amirka, da gaske yake kan batutuwan da ya fada lokacin yakin neman zabe.