Trump ya sallami Antoni Janar ta Amirka. | Labarai | DW | 31.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya sallami Antoni Janar ta Amirka.

Trump ya sallami Antoni Janar kuma babbar lauyar gwamnati saboda kin yin biyayya ga umarninsa na hana shigar yan wasu kasashe cikin kasar Amirka.

Shugaban Amirka Donald Trump ya kori Antoni Janar din kasar wacce ta ki ta amincewa ta yi aiki da sabuwar dokar da ya dauka wacce ta tanadi haramta wa 'yan wasu kasashen bakwai akasarinsu na Musulmi shiga kasar ta Amirka. 

A cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar ta bayyana Sally Yates wacce dama jami'ar tsohuwar gwamnatin Obama ce da ke rike da mukamin Antoni Janar kuma babbar lauyar gwamnati ta Amirka a matsayin wucen gadi, da cin amanar ma'aikatar shari'a kasar, bayan da ta umurci babban alkalin kasar da kar ya yi biyayya ga wannan doka da Shugaba Trump ya dauka. 

Tuni dai Shugaba Trump ya nada Dana Boente a matsayin Antoni Janar na riko kafin majalisar dattawan kasar ta tabbatar da nadin Sanata Jeff Sessions. Kazalika Shugaba Trump ya maye gurbin shugaban hukumar shige da fice da kuma kwastam na riko Daniel Ragsdale wanda shi ma jami'in tsohuwar gwamnatin Obama ne, da Thomas Homan.