Trump ya sake kai ziyara Texas | Labarai | DW | 02.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump ya sake kai ziyara Texas

A dazu ne shugaban Amirka Donald Trump ya isa jihar Texas wadda ta gamu da ibtila'i na ambaliyar ruwa da ya yi sanadin rasuwar mutane da dama da kuma raba dubban mutane da muhallansu.

Trump din dai ya isa Texas din ne tare da mai dakinsa Melania kuma tuni suka isa birnin Houston don zantawa da al'ummar da abin ya shafa inda ya shiga sahun masu taimakawa wajen rabon abinci kana ya kewaya wuraren da ambaliyar ta yi ta'adi. A 'yan kwanakin da suka gabata shugaban ya sha caccaka bayan da ya ziyarci Texas din cikin makon jiya amma kuma bai kusanci wanda wanda wannan matsala ta shafa ba domin jajanta musu tare da tattaunawa da su kai tsaye ba.