1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya sa kudin fito kan shigo da karafa

Abdullahi Tanko Bala
March 1, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya nanata kakkausar suka akan abun da ya kira rashin adalcin wasu kasashe wajen cinikayya.

https://p.dw.com/p/2tYNM
USA Präsident Donald Trump
Hoto: Getty Images/AFP/M. Ngan

Shugaban Amirka Donald Trump yace daga mako mai zuwa Amirka za ta sanya kudin fito na kashi 25 cikin dari akan kamfanoni da suka shigo da karafa daga waje yayin da za sanya harajin kashi goma cikin dari akan farin karfe.

A wani taro da ya yi da wakilan masu masana'antu a fadar White House, Trump ya ci alwashin sake habaka masana'antun tama da karafa na Amirka yana mai cewa an shafe shekaru da dama ana zaluntar kamfanonin karafa na Amirka.

Tun da farko a wani sako da ya wallafa a shafinsa na tweeter Trump bai ambaci kowace kasa ba , amma kalaman nasa na zuwa ne yayin da mai bai wa shugaban China shawara kan tattalin arziki Liu He da 'yan tawagarsa suke shirin ganawa da sakataren kudin Amirka Steven Mnuchin a fadar White House.