1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump: Shirin ganawa da Kim ya kammala

Ahmed Salisu
June 7, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya ce sun shirya tsaf domin tattaunawa da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un a kasar Singapore ranar Talatar makon gobe.

https://p.dw.com/p/2z6bY
Kombobild von Kim Jong Un und Trump

Shugaban ya ambata hakan ne dazu lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a fadar White House lokacin da ya marabci firaministan Japan Shinzo Abe inda shugabannin za su tattauna kan batutuwa da dama ciki kuwa har da dangantakar Amirka da Koriya ta Arewa. Shugaban na Amirka ya ce har yanzu kasarsa na nan kan bakanta na ganin Arewa ta yi watsi da shirinta na nukiliya inda ya kara da cewar in hakan ba ta yiwu ba to Washington za ta kasance ba ta da zabi illa ta kara kakakabawa Arewan din takunkumi.