Trump da shirin nukiliyar Koriya ta Arewa. | Labarai | DW | 03.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Trump da shirin nukiliyar Koriya ta Arewa.

Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce a shirye ya ke ya yi gaban kansa wajen kalubalantar shirin nukiliyar Koriya ta Arewa ba tare da taimakon kasar Chaina ba.

Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce a shirye ya ke ya yi gaban kansa wajen kalubalantar shirin nukiliyar Koriya ta Arewa ba tare da taimakon kasar Chaina ba. Jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya wacce ta wallafa wannan labari ta ruwaito Shugaba Trump na cewa idan har kasar Chaina ba ta magance matsalar Koriya ta Arewa ba, to kuwa shi zai shawo kanta shi kadai. 

Wadannan kalamai na Shugaba Trump na zuwa ne lokacin da ya rage kwanaki uku ya karbi bakuncin shugaban kasar ta Chaina Xi Jinping wanda za kai wata ziyarar aiki ta kanaki biyu Alhamis da jumma'a a kasar ta Amirka. 

Dama dai tun a jiya Lahadi jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta bayyana cewa Amirka na da niyyar matsa wa Chaina lamba kan ta dauki mataki a game da shirin nukiliyar Koriya ta Arewa.