1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Toshe yankin Gaza

Ƙasashen duniya sun soki Isra'ila, bisa kisan mutanen da suke ɗauke da kayan agaji zuwa Gaza

default

Zauren kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya

Kusan bai ɗaya kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah wadai da farmakin da Isra'ila ta yi wa ayarin jiragen ruwa dake ɗauke da kayan agaji izuwa Gaza, domin tallafa al'ummar yanken da Isra'ila ta kange. Kwamitin majalisar yace kisan fararen hula dagangan ba abune da za'a lamunta da shi ba.

Ba kasafai bane ake yiwa Isra'ila tofin ala tsine irin wannan ba, musamman daga ƙasashen yamma. To amma wannan karon martanin yana da zafi, kusan daga ko'ina, sai dai ƙasar Turkiya ita ce tafi ɗaukar zafi bisa matakan da sojan Isra'ila suka yi. Inda suka janye jakadansu daga Isra'ila nan take, kana suka gayyaci jakadan Isra'ila dake ƙasar don nuna ɓacin ransu. Ministan harkokin wajen ƙasar ta Turkiya Ahmet Davutoglu yace

"Wannan baƙar rana ce ga tarihin bil'adama, kuma batun banbancin 'yan ta'adda da cikakkakiyar ƙasa an share shi.

Daga cikin tawaggar dake cikin jirgin ruwanda sojin da Isra'ila suka farma, akwai ƙungiyoyi da 'yan majalisun dokoki daga ƙasace daban daban, musamman daga Turai da Amirka, aƙalla akwai Jamusawa 10 ciki. Don haka ministan harkokin wajen na Turkiya ya ƙara da cewa.

"Wannan abun yana dai dai da yan fashin teku. kesan ƙiyashine da wata ƙasa ta yi. Don haka Isra'ila bai kamaci duniya ta ɗauke ta a matsayin ƙasa ba"

Kusan dukkan wakilan kwamitin sulhun 15, suka kaɗa ƙuri'ar kafa wani kwamitin gaggawa mai zaman kansa wanda zai binciki, ta yaya Isra'ila ta shiga tsakiyan teku wanda ba mallakar ta bane, domin lamarin ya faru a tekun ƙasa da ƙasa, amma har ta kai ga kisan mutane. Kana kwamtin sulhu ya buƙaci da a kawo ƙarshe kange yanken zirin Gaza da akayi na tsawon shekaru uku. kamar yadda sakataren majalisar mai kula da al'amuran siyasa yace.

"Da an kaucewa wannan zubar da jini, indan da Isra'ila ta kawo ƙarshen kange war marar gado, wanda duniya bata lamunta da ita ba, da ta ke yi wa zirin Gaza"

To sai dai muƙaddashin jakadan Isra'ila a Majalisar Ɗinkin Duniya Daniel Carmon yace duk wannan batun siyasace kawai, bawai Gaza ta rasa wani abun jinƙai bane.

"A ko wacce rana ana kai kayan a Gaza, ba'a buƙatar kayan agaji a yankin"

Ita ma dai ƙasar da Isra'ila ke rawa da bazarta wato Amirka, ta maida martani a fakaice inda jakadanta a majalisar yace da kamata ya yi a kai kayan agajin ta tashar jiragen ruwan Isra'la, inda daga nan bi ta motocin don isar da shi Gaza.

Amma shi kuwa jakadan Palasɗinu ya kwatanta abinda sojin Isra'ila suka, da cewa gungun mutanene da suka aikata laifin yaƙi. Yayin da sakatare janar na majalisar Ban Ki-moon, yace ya kaɗu da zubar da jinin bayin Allah wanda Isra'ila ta yi. Kana ya buƙaci Isra'ila da ta kawo ƙarshen toshe yankin Gaza da take yi

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Lena Bodewein

Edita: Umaru Aliyu