Toshe shirye-shiryen harshen Amharish | Siyasa | DW | 29.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Toshe shirye-shiryen harshen Amharish

A Ethiopiya an sake toshe Muryar Jamus mai fafatukar kare haƙƙin Bil Adama.

default

An yi tir da matakin da hukumomin Ethiopiya suka ɗauka na toshe hanyoyin kama shirye-shiryen sashen Amharish na Deutsche Welle

A daidai lokacin da hankula suka karkata wajen jiran sakamakon zaɓen da aka shirya, sai kwatsam babu zato babu tsammani, gwamnatin Ethiopiya ta toshe hanyoyin sauraron shirye-shiryen Rediyo Deutsche Welle na harshen Amharish.

Cimma dai wannan ba shi ne karon farko ba, da gwamnatin Ethiopiya ta rufe tashoshin samar da shirye- shiryen Rediyo Deutsche Welle sashen Amharish da ma na Muryar Amurika.Ta wannan hanya wai tana ga za ta iya rufe bakin kafofin sadarwa na ƙetare dake tsage gaskiyar yadda al´amura ke gudana a cikin ƙasar.

A lissafin da ta yi shekarar da ta gabata, Ƙungiyar ´yan jarida ta ƙasa da ƙasa ta jera Ethiopiya a matsayi na 140 ta fannin take yancin ´yan jarida. Hukumomin ƙasar sun yi suna wajen ƙuntatawa kafofin sadarwa masu zaman kansu.

A yayin da yake maida martani ga matakin, shugaban Deutsche Welle Erick Bettermann ya bayana taikaici:

"Abun mamaki ne, ɗaukar wannan mataki, kwanaki ƙalilan bayan zaɓen ´yan majalisar dokoki. Sam matakin ya saɓawa dokokin ƙasa da ƙasa, kuma ya ma saɓawa 'yancin bani Adama, hasali ma 'yancin samun labari a duniya".

A shekara 2007 da 2008 ma, gwamnatin Ethiopiya ta toshe hanyoyin samar da shirye-shiryen sashen Amharich na Deutsche Welle, a matakin mai kama da riga kafi ga mamayen da sojojin Ethiopiya suka yi a ƙasar Somaliya da kuma ƙaruwar barazanar yaƙi tsakanin Ethiopiya da Eritriya.

A cewar Ambroise Pierre shugaban Ƙungiyar ´yan jarida ta ƙasa da ƙasa wato Reporters sans Frontiéres ya bayyana cewar matakin na Firaminista Meles Zenawi, ba zai rasa nasaba da siyasa ba. Bayan ya sa kafofin sadarwa na cikin gida sun yi shiru, yanzu kuma ya juwa ga na ƙetare to amma hakan ba za ta saɓu ba:

"Abin ya dame mu matuƙa. Mun rubuta wasiƙa ga hukumomin Ethiopiya, inda muka yi masu kira da cewar su sakarwa kafofin sadarwa mara su yi aikinsu, to amma sun yi kunnen uwar shegu, ga shi yanzu abin har ya kai da Deutsche Welle".

Tun shekara ta 2005 gwamnatin Ethiopiya ta kafa ƙafon zuƙa ga tashar Deutsche Welle dalili da rahotannin da ta yaɗa game da mace-mace mutane fiye da 200 da suka biwo bayan rikicin zaɓe.

Ƙarewa da ƙarau, har sai dai da gwamnatin Meles Zenawi ta kai ƙaran Deutsche Welle gaban Majalisar Dokokin Bundetsag dake birnin Berlin. To sai dai binciken ƙwaƙƙwaf tare da fassara kalamomin rahotannin, sun wanke Deutsche Welle daga zargin, to amma duk da haka, sai a shekara ta 2008 ne shugabar gwamnati Angela Merkel ta ciwo kan hukumomin Ethiopiya su cire takunkumin da suka sakawa shirye-shiryen Deutsche Welle.

Shugaban Deutsche Welle Erick Bettermman, ya bayyana wajibcin magance wannan matsala da ta sake kunno kai cikin gaggawa, domin shirye-shirye rediyo, tamkar makaranta ce ga masu sauraro.

Mawallafa: Ludger Schadomsky / Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Mohammad Nasiru Awal