1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tony Snow ya zama sabon kakakin fadar gwamnatin Amurka

April 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6j

Shugaba George W Bush na Amurka ya nada jagoran gidan Radion Fox,Tony Snow a matsayin sabon sakataren yada labarun fadar gwamnati ta White house,a wani abunda ke zama tankade da rairaya na maaikatan fadarsa.A taron manema labaru daya gudanar yau shugaban na Amurka,yace ya zabi Mr Snow saboda sanin irin hazakarsa cikin ayyaukansa,wanda ya hakikance cewa zai taimaka matukas gaya a harkokin aiki na fadar gwamnati ta white house.

Mai shekaru 50 da haihuwa kuma mai raayin yan mazan jiya Tony Snow,zai maye gurbin Scott McClellan,wanda ya sanarda yin murabus daga mukamin kakakin gwamnatin Amukar a makon daya gabata,wanda ke bangaren canje canjen maaikatan fadar gwamnatin da shugaban maaikata Josh Bolten ke gudanarwa.A jawabinsa na amincewa da wannan mukami,Mr Snow ya godewa shugaba Bush da wannan dama daya bashi da kuma dalilansa na amincewa.

A matsayinshi na mai tsattsauran raayi,Snow yasha sukan tsare tsaren gwamnatin Bush musamman harkokin kashe kudi.