Tony Blair yayi murabus | Labarai | DW | 10.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tony Blair yayi murabus

Prime minista Tony Blair na kasar Britania zai sauka daga karagar mulki ranar 27 ga watan yuni mai kamawa ,idan Allah ya kaimu.A yau ne ya gabatar da wannan sanarwa a mazabarsa dake Sedgefield,dake yankin arewacin Engla.Yayi amfani da wannan dama wajen neman gafara daga wajen magoya bayansa bisa abunda ya kira gazawarsa,sai dai yace a koda yaushe yana gudanar da ayyuka ne ,da a ganinsa ya dace da kasar baki daya.Ansaran Mr Gordon Brown shine wanda zai gaji Tony Blair a matsayin shugaban jammiiyyar Labour da da kuma matsayin prime minista.