Tony Blair ya yi murabus daga shugabancin Britaniya | Labarai | DW | 27.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tony Blair ya yi murabus daga shugabancin Britaniya

Hausawa kan ce wai dunia rawar yan mata, na gaba ya koma baya, haka dai wannan al´amari ya kasance ga tsofan Praministan Britania, Tony Balir, wanda a yau ya sauka daga mukamin sa, bayan shekaru 10, ya na jan ragamar mulkin wannan ƙasa.

Sarauniya Elisabeth ta Engla ta amince da wannan murabus, kuma ba da wata wata ba, ta naɗa Gordon Brown a matsayin saban Praminista.

Brown ya gabatar ta ɗan taƙaittacen jawabi, inda ya bayyana burin da ya ɗauke da shi.

Gordon Brown ya alƙawata tsamo mata da maza gwarzaye wanda za su duƙufa wajen cimma wannan buri.

Gobe a ke sa ran Gordon Brown,zai bayyana sunayen membobin gwamnatin.