Tony Blair ya sha alwashin jawo hankalin duniya domin taimakawa nahiyar Afrika. | Labarai | DW | 13.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tony Blair ya sha alwashin jawo hankalin duniya domin taimakawa nahiyar Afrika.

P/M Britaniya Tony Blair ya lashi takobin cigaba da jawo hankalin kasashen duniya su taimakawa kasashen Afrika. A wajen wani taron shugabanni masu raáyin gaba dai gaba dai da aka gudanar a birnin Johannesburg ta Afrika ta Kudu, Blair ya nanata cewa akwai bukatar kasashe masu arziki na duniya su cika alkawuran da suka yi na baiwa Afrika gudunmawar jin kai da kyautata huldar cinikayya da kuma bada tallafi ga ayyukan kiyaye zaman lafiya. Bugu da kari Tony Blair ya yi fatali da zargin cewa kasashen na duniya sun yi watsi da batun da ya shafi Afrika a tsarin jadawalin su tun bayan da Britaniyan ta sauka daga shugabancin karba karba na kungiyar kasashe masu cigaban masanaántu na duniya G8.