1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tony Blair ya ce halin da ake ciki a Darfur ba abin amincewa ba ne

September 16, 2006
https://p.dw.com/p/BujQ

FM Birtaniya Tony Blair ya bayyana mawuyacin halin da ake ciki a lardin Darfur mai fama da rikicin a yammacin Sudan da cewa ba abin karbuwa ba ne. A saboda haka Blair ya yi kira da aka kara matsawa gwamnatin birnin Khartoum da kuma ´yan tawaye lamba. Da farko ministocin harkokin KTT sun nuna damuwa game da karuwar tashe tashen hankula a lardin na Darfur. A cikin wata sanarwa da suka bayar a birnin Brussels ministocin sun yi kira da a gurfanad da wadanda ke da hannun wajen kisan kare dangi da wahalhalun da ake fuskanta a Darfur din, a gaban shari´a. A kuma can birnin Washington shugaban Amirka GWB ya yi Allah Wadai da adawar da gwamnatin Sudan ke nunawa shirin girke dakarun MDD a Darfur.