1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tony Blair ya bayyana aniyar sauka daga kujera mulki.

September 7, 2006
https://p.dw.com/p/BukK

A sakamakon dambarwar siyasar da ke wakana a ƙasar Britania, Praminista Tony Blair, da ke shan suka, daga yan adawa, da jama´iyar Labor, da ya ke jagoranta, ya bayana aniyar sa,ta sauka daga muƙamin sa, nan da shekara guda mai zuwa.

Blair ya bayana hakan ,a wani taron manema labarai da ya kira yau alhamis.

Ya bada kai bori ya hau, ga matsin lambar da ya ke fuskanta a halin yanzu , inda da dama daga na hannun damar sa, su ka yi murabus domin nuna adawa da yanayin gudanar da mulkin sa.

Saidai Blair, bai bayana ba, a zahiri ranar da zai sauka.

Wannan mataki na a yada ƙashi a huta da kuɗa, da Tony Blair ya ɗauka, zai ba muƙƙadashin sa, Gordon Brown ,damar maye kujeran Praminista.