Toka, saboda aman wuta na dutse a ƙasar Iceland | Labarai | DW | 15.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Toka, saboda aman wuta na dutse a ƙasar Iceland

Zirga - zirgar jiragen sama na samun cikas sakamakon wani dutsen dake aman wuta a Iceland

default

Wata mummunar toka sakamakon wani dutsen dake aman wuta a ƙasar Iceland ta tarnuƙe a sararin samaniyar wasu ƙasashen Turai, ta kuma yi sanadiyyar soke jigilar jiragen sama da dama a nahiyar Turai, da kuma wasu ƙasashen duniya. Kimanin ƙasashe takwas ne suka soke tafiye tafiye ta sararin samaniyar su saboda gargaɗin da aka yi na samun cikas a zirga - zirgar jiragen. Ƙasashen kuwa sun haɗa ne da Birtaniya da Holland da kuma Beljiam. Hukumar kula da sararin samaniya a Turai ta yi gargaɗin cewar, akwai yiwuwar fa'ɗaɗa haramcin zirga - zirgar i zuwa ƙasashen Jamus da Faransa. Tokar aman dutsen dai, na yin tafiyar da saurin ta yakai kilomita 35 a cikin sa'a guda a kudu maso gabashin Turai. A ranar wannan Larabar ce, dutsen ya fara aman wuta a yankin kudancin Iceland - a karo na biyu cikin wata guda, bayan daya yi tsawon shekaru 200 ba tare da ya yi hakan ba. Hukumomi na fargabar cewar, akwai yiwuwar ya sake yin aman, wanda kuma zai janyo cikas ga zirga - zirgar jiragen sama - har na tsawon mako ɗaya.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Yahouza Sadissou