1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za mu iya daukar kowane mataki,

March 17, 2017

Daukar matakin soji a kan Koriya Ta Arewa na daga cikin zabi abin dubawa inji sakataren harkokin wajen Amirka idan har ba ta yi watsi da manufarta na kera makamin nukiliya ba.

https://p.dw.com/p/2ZQ1r
Südkorea Rex Tillerson in Korea - an der Grenze
Hoto: picture alliance/dpa/L. Jin-Man/AP POOL

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson yace hakurin Amirka a kan Koriya Ta Arewa ya gushe, yana mai cewa ana iya daukar kowane irin mataki ko da kuwa ya hada da amfani da karfin soji. 

" Wajibi ne Koriya ta arewa ta fahimci cewa hanya daya tilo a gareta ta samun kyakkyawar makoma da  cigaban tattalin arziki shine ta yi watsi da akidarta ta kera makaman nukiliya da sauran makaman kare dangi."

Tillerson yayi wadannan kalamai ne a taron manema labarai na hadin gwiwa da ya gudanar tare da takwaransa na Koriya ta Kudu Yun Byung, yace babu wani lokaci na cigaba da tattaunawa da Koriya ta Arewa. Yana mai nuni da cewa an kwashe shekaru ashirin ana tattaunawa da ita ba tare da biyan bukata ba.

Sakataren harkokin wajen na Amirka ya kuma ce babu gudu ba ja da baya a kudirin Amirka na kafa cibiyar kakkabo makamai masu linzami a Koriya ta kudu domin kariya daga barazanar Koriya ta arewa.

China dai na adawa da wannan mataki tana mai cewa zai kara rura wutar zaman dar dar a yankin.