1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Theresa May na ziyara a kasar Turkiyya

Salissou Boukari
January 28, 2017

Firaministar Birtaniya Theresa May tana birnin Ankara na kasar Turkiyya a wata ziyara da ta soma a ranar Asabar, a wani mataki na neman karfafa huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/2WZ8J
Theresa May und Erdogan in Ankara
Firaministar Britaniya Theresa May da Shugaba Erdogan na Turkiya Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo

Madame May ta gana da Shugaban kasar ta Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da kuma Firaministan kasar Binali Yildirim. Hakan dai ya nuna bambamcin da Firaministan ta Birtaniya take da shi tsakaninta da sauran shugabannin kasashen Turai da suke nuna ja baya wajen zuwa kasar ta Turkiyya, tun bayan da ta soma kame-kamen mutane bayan yunkurin juyin mulkin da aka yi na ranar 15 ga watan Yuli da ya gabata.

Da farko dai kaman yadda yake a al'ada sai da Madame May ta ajiye furanni ga kabarin Atatürk kafin ta fice ya zuwa fadar shugaban kasa. Wannan ziyara na zuwa ne kwana daya bayan wadda ta kai a kasar Amirka, inda ta kasance shugaba ta farko ta wata kasa da ta gana da shugaban Amirka Donald Trump bayan da aka rantsar da shi. Kasar ta Turkiyya dai da ke neman shiga kungiyar Tarayyar Turai tun daga shekara ta 1980, a baya ta yi ta daukan kasar ta Birtaniya a matsayin mai goya mata baya kan wannan batu.