Teheran zata mayar da martani kan Isra´ila idan aka kaiwa Iran hari | Labarai | DW | 19.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Teheran zata mayar da martani kan Isra´ila idan aka kaiwa Iran hari

Iran ta ce ta tsara wani shiri don mayar da martani akan Isra´ila idan aka kai mata hari. Wani mukaddashin rundunar sojin saman Iran ya ce jiragen saman yakin Iran masu dauke da bama-bamai ka iya kai harin daukar fansa a yankunan Isra´ila. Wadannan kalaman sun zo ne bayan kasashen Amirka da Faransa suka yi ta nanata wani gargadi kan shirin nukiliyar gwamnatin birnin teheran. Wani jami´i a ma´aikatar harkokin wajen Isra´ila ya ce dole yankin GTT ya razana a dangane da wannan sanarwa ta Iran. Ita kuma fadar White House a birnin Washington cewa ta yi kalaman ba su dace ba kuma ba zasu taimaka ba. Kasashen China da Rasha sun yi tir da furucin ministan harkokin wajen Faransa Bernard Kouchner wanda ya ce ba a kawad da yiwuwar daukar matakin soji kan Iran ba don hana ta kera makaman nukiliya.