1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar mdd zataje Darfur

January 26, 2007
https://p.dw.com/p/BuTG

Wata tawagar bincike na mdd akarkashin jagorancin Jody William da ta taba karbar lambar yabo adadngane da kokarin ta na samar da zaman lafiya ,zata ziyarci kasar Sudan domin binciken zarkin take hakkin jamaa da ake cigaba dayi a lardin Darfur.A shekarata 1997 nedai Madam williams ta samu wannan olambar yabo ta nobel ,adangane da yaki da matsalolin nakiyoyui da ake binnewa a karkashin kasa.Bugu da kari tawagar zata kuma kunshi wakiliyar dake ruwaito batutuwan kare hakkin jamaa ta musamman dake sudan Sima Samar,inji kungiyar kare hakkin jamaa ta mdd.Shugabar kungiyar kuma jakadar Mexico a MDD Luis Alfonso de Alba,ta kuma zabi wasu jakadu guda biyu daga Gabon da Indonesia ,wadanda zasu hade a ayarin masu gudanar da binciken a Darfur.