Tawagar kungiyar taraya Afrika ta kasa cimma burin nada saban Praminista a kasar Kote Divoire
November 23, 2005Shugaban kungiyar Gammaya Afrika, Olesegun Obasanjo, da na kungiyar ECOWAS, Tanja Mamadu, da kuma shugaban Afrika ta kudu Tabon Mbeki, da ke shiga tsakani a rikicin Kote Divoire, da su ka kai ziyara jiya a wannan kasa, sun kasa cimma burin su, na zaben saban Praminista.
Tawagar shuwagabanin, ta tantana da gwamnatin kasar Kote Divoire, da yan adawa, da kuma yan tawaye, a game da wannan batu mai sarkakiya.
Bayan tankade da reraye sun cimma daidaito na samun yan takara 2, daga jerin jimilar mutane 16 da a ka gabatar da sunayen su , wanda daga cikin su ya cencenta a tsamo saban Praministan, da bangarori baki daya za su yi masa mubai´a.
Saidai a cewar shugaban Obasanjo, daga wannan yan takara 2 ,babu wanda ya cika sharrudan da za su gamsar da kowa.
A game da haka tawagar shuwahabanin kasashen zata sake komawa nan da kwanaki 10 masu zuwa, domin ci gaba da tantanawa.
Idan za a iya tunawa ,a satin da ya wuce, yan tawaye , sun yi watsi da jerin sunayen 16, da a ka gabatar masu, dalili da babu sunan shugaban su Guillaume Soro a ciki.