1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Dunia na ziyara a Sudan

June 6, 2006
https://p.dw.com/p/Buv9

Tawagar komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, na ci gaba da ziyara a ƙasar Sudan.

Tawagar, ta yi ganawar farko, da shugaban kasa Omar El Beshir, a game da rikicin yankin Darfur.

Bayan yarjejeniyar birnin Abuja tsakanin yan tawaye, da gwamnatin Sudan, Majalisar Ɗinkin Dunia, bisa gayatar Ƙungiyar Taraya Afrika,ta yanke hukunci aika dakarun shiga tsakani, domin tabbatar da wannan yarjejeniya.

To saidai, har ya zuwa yanzu, hukumomin Khartum ,na nuna ɗari ɗari, na amincewar karɓar dakarun shiga tsakanin.

A na sa ran a sakamakon wannan ziyara, tawagogin 2 su cimma daidaito akan batun.

A mataki na gaba, tawagar komitim sulhun, za ta ziyarci ƙasashen Tchad, da Ethiopia, da kuma Jamhuriya Demokradiyar Kongo ,inda a nan ma, wasu rigingimun, ke ci gaba da wanzuwa.