Tawagar France ta ziyarci Niger a game da rikicin tawaye | Labarai | DW | 04.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tawagar France ta ziyarci Niger a game da rikicin tawaye

Ƙaramin ministan ƙasar France mai kulla da hulɗoɗi da ƙetare Jean Marie Bockel ya fara rangadi a Jamhuriya Niger.

A yau ya gamna da shugaban ƙasa Tanja Mamadu, inda su ka tanatanna a kann batutuwa daban-daban da su ka jiɓancin hulɗoɗi tsakanin Paris da Niamey, mussamman rikicin baya-bayan nan na kampanin Areva mallakar France.

Idan dai ba a manta, a makon da ya gabata, gwamnatin Jamhuriya Niger, ta kori shugaban kampanin Areva wanda ta ke zargi ta tallafawa ƙungiyar MNJ baya.

A yayin da ya kai rangadi a wasu ƙasashen Afrika shugaban France Nikolas Sarkozy, ya alkawarta sulhunta Niger da Kampanin Areva.

Bisa dukan alamu ya cimma nasara, domin tunni an rattaba hannu a kan sabuwar yarjeniyar tsakanin Areva da gwamnatin Niger.

Kazalika, Jean Marie Bockel ya bayyana gamsuwa da tantnawar da da ya yi yau, da shugaban ƙasa Tanja Mamadu.

Wannan ziyara ta biwo bayan wadda ministar harakokin wajen Niger Aishatu Mindaudu ta kai ƙasar France a wannan makon.