Tawagar ECOWAS ta yaba zaɓen Jamhuriyar Benin | Labarai | DW | 21.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tawagar ECOWAS ta yaba zaɓen Jamhuriyar Benin

Tawagar ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta yamma, wato CEDEAO, ko kuma ECOWAS, da ta sa iddo, ga zaɓen shugaban ƙasa zagaye na 2,a Jamhuriya Benin, ta bayyana rahoton ta, a game da yadda wannan zaɓe ya wakana.

Tawagar tace an gudanar da zaɓen, cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da kiyaye haƙoƙin demokaradiya.

A wani taron manema labarai da ta shirya, tawagar ECOWAS, ta yi yabo ga hukumar zaɓe mai zaman kanta, a game da ƙoƙarin da ta yi ,na shirya aiki tsabttace, duk da gardandamin da aka sha yi, tsakanin hukumar zaben da gwamnati, a game da tsaida ranar zagayen na 2.

Zaɓen na ranar lahadi ,da ta wuce, inji tawagar CEDEAO, har ma ya fi zagaye na 2 tsari, hakan ya nuna cewar, al´ummomin ƙasar Benin, sun zama abin koyi ,ta fanin demokaradiya.

A ƙarshe sannarwa da CEDEAO ta hiddo, ta gayyaci yan takara 2, da su ka shiga zaɓen, da su amince da sakamakon da hukumar zaɓe mai zaman kanta, zata bayyana, na da ɗan lokaci mai zuwa, su kuma haɗa kai, domin hidda Jamhuriya Benin, daga matsalaoli iri daban-daban da ta ke fuskanta.